‘Yansandan Najeriya sun ceto yara 23 da ake shirin ‘siyar’ da su a Abuja

‘Yansandan Najeriya sun ceto yara 23 da ake shirin ‘siyar’ da su a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar kuɓutar da wasu yara ashirin da uku daga wani gidan marayu da ke Unguwar Kubwa a Abuja, babban birnin ƙasar wanda ake zargin ana fakewa da shi ana hada-hadar safarar yaran har zuwa ƙasashen waje.

Cikin yaran dai har da ‘yan shekara ɗaya zuwa uku, wasun su kuma sun kwashe kimanin shekara uku a gidan.

DSP Mansir Hassan, shi ne jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriyar a jihar Kaduna, ya ce jami’an rundunar sun karaɗe jihohi goma sha ɗaya a ƙoƙarin bankaɗo gidan da kamo wadan da suke da hannu a satar yara, tare da hadahadar siyar da su.

Cikin yara bakwan da suka ceto akwai maza biyu da mata biyar.

Ya ce ‘akwai yaran wadan da ake sace wa daga gidajen iyayensu, wasu kuma a wurare daban-daban, mun yi nasara wajen kama mutum 8, sannan mun ceto yara biyu wadan basu wuce shekaru biyu ba, sannan mun kuma ceto karin wasu mutum bakwai, iyaye na ta gane ‘ya’yansu, ciki har da wata da aka sace shekara uku da suka gabata mai suna Debora’, in ji DSP Mansir Hassan.

Mansir Hassan din ya ce sun gano yara ne a wani gidan marayu da ke Kubuwa wato ‘Debora Orphanage Home’ a babban birnin Abuja, baya wasu bayanai da suka samu daga wajen mutum takwas sin da suka kama, sun sami yara 23, 17 daga cikin su sun sami bayanai akansu suka barwa gwamantin Abuja, yayin da ya sauna bakwan sune suka koma da su.

‘Akan dai hada guwai ne da wasu daga cikin ma’aikata bata garin da ke aiki a irin wadannan gidajen marayu, kuma a wasu lokutan fakewa suke yi da gidan marayu a sai su ringa siyar da yara, kamar yadda muka samu a wannan gida.

Sai a siyar da yaro miliyan daya, kamar yadda aka biya na wani yaro naira miliyan daya da dubu dari takwas, dayan kuma dubu dri bakwai, su wadan nan yaran ana kokairn yin safarar su ne’, in ji DSP Mansir Hassan.

Ya kuma ce, ‘wasu daga cikinsu kuma ana rainonsu ne a bautar da su, wasu kuma sassan jikinsu ake siyarwa akwai wani yaro da aka ce na kai shi Umahiya, da muka je sai aka ce yana taraba, kuma dukkan yaran an sauya musu suna. A wani lokacin ma daga kudancin Najeiryar suke, hakan shi ke nuni da cewar safararsu ake yi’, in ji kakakin yan sandan na Kaduna.

Dsp Mansir Hassan ya ce tuni suka aike da wadan da ake zargi zuwa kotu yayin da wasu daga cikinsu ke ci gaba da amsa tambayoyi, kuma ana ci gaba da samun karin bayanai.

Matsalar satar kanan yara a Najeriya dai ba sabon alamari ba ne, wanda ko a shekarun da suka gabata na sha fama da irin wannan matsala a jihar Kano da ke makwabtaka da jihar Kadunan, inda wasu iyaye suka koka kan yadda aka sace yaansu su taa, da suke zargin an sace su tare da siyar da su a jihar Anambra da ke udancin kasar, wand bayan bincike, aka gano tare da dawo da yaran wajen iyayensu.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *