Wasu yankunan Borno na ‘kuɓucewa’ daga hannun gwamnati – Zulum

Wasu yankunan Borno na ‘kuɓucewa’ daga hannun gwamnati – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ƙungiyar Boko Haram ke sanyawa jihar ke “rasa wasu daga cikin yakunanta.”

Zulum ya bayyana haka ne yau Talata a lokacin taron lamurran tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

A cikin jawabin da ya gudanar, Zulum ya ce “Yayin da nake wannan jawabi a yau, abin takaici shi ne sabbin hare-haren Boko Haram da satar mutane da suke yi a yankuna da dama a a kowace rana, ba tare da an ƙalubalance su ba, na nuna cewa jihar Borno na rasa ƙasarta”.

“Kamar yadda kuka sani, gwamnatina na taimaka wa sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da Boko Haram da sauran ƴan ta’adda, lamarin da ya sanya aka samu sauƙi a cikin shekaru uku da suka gabata, amma abin takaici ne na shaida muku cewa hare-hare na baya-bayan nan da tarwatsa sansanin soja a Wajirko da Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da wasu sauran kashe-kashen fararen hula da jami’an tsaro a baya-bayan nan abin damuwa ne, kuma koma-baya ne ga jihar Borno da kuma yankin Arewa maso Gabas.”

A saboda haka ne gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi a ƙoƙarinta na tabbatar da tsaro da kuma yaƙi da ƙungiyar ta Boko Haram.

A baya-bayan hare-haren Boko Haram na ƙara ƙamari a jihar, lamarin da ya haifar da asarar rayukan fararen hula da kuma jami’an tsaro.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *