SHEKARA 7 BAYA SALLAH, YA KASHE MUTANE DA DAMA, YA KASA BARCI

SHEKARA 7 BAYA SALLAH, YA KASHE MUTANE DA DAMA, YA KASA BARCI

Acikin Hirar da akayi dashi ya shaidawa yan jarida cewa yafi shekara 7 baya sallah

Shi dan fashin waya ne Kuma babu abunda ya keyi da kudin nan sai neman mata, baya shaye shaye karshe dai a gidan karuwai ya tare da zama fiye da wata 6 kullum kudin daki kawai 6k a ke biya acikin Sabon garin dake jahar Kano.

Abdullahi Haruna Kiyawa yana tambayarsa iyayensa nada rai ya ce eh amma suna masa fada yace eh amma baya zama tare dasu, ankara tambayarsa matakin karatunsa yace firamari kawai yayi babu ilimin addini da boko balantana ya iya karatun sallah.

Idan ya sato waya mai tsada ta kimanin kudi N750k Naira N150k ake bashi a farm center cikin garin Kano.

Satar karshe da yayi wanda ya sokawa wani mutum wuka a wuya sau biyu, ya dauke masa waya mai kimanin kudi 140k infinix Hot40i wanda ya kai aka bashi N40k kuma wanda ya siya wayar yaga akwai miliyan daya da wasu dori acikin account din wayar da aka sato.

Ya ce duk idan ya kwanta baya iya barci sai mugun mafarki, idan yana tsaye zai dunga jin jiri na daukarsa.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *