Najeriya ba ta cikin ƙasashen da Saudiyya ta daina bai wa biza – Gwamnatin Najeriya

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da Saudiyya ta daina bai wa biza – Gwamnatin Najeriya

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta musanta cewa ƙasar na cikin jerin ƙasashe da Saudiyya ta hana ba su biza daga 13 ga watan Afrilu.

Kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar na yin ƙarin bayanin ta bakin mataimakinsa na musamman kan kafofin yaɗa labarai, Alkasim Abdulkadir, ranar Litinin.

Ministan ya ce Saudiyya ta tabbatar musu cewa jerin sunayen da ke nuna Najeriya na cikinsu, wanda kuma aka dinga yaɗawa a shafukan sada zumunta, ba na gaskiya ba ne.

“Hukumar Saudiyya ta tabbatar babu wani umarni mai kama da haka, dokokin da aka saka a hyanzu sun shafi aikin Hajji ne kawai. A gane cewa, dokokin sun shafi masu bizar yawon buɗe ido ne kawai a lokacin aikin Hajji,” a cewarsa.

Bisa ƙa’idojin, an haramta wa masu bizar yawon buɗe ido yin aikin Hajji, ko shiga Makkah tun daga 29 ga watan Afrilu zuwa 11 ga Yuni (ko kuma 1 ga watan Zul Ƙida zuwa 14 ga Zul Hijjah na kalandar Musulunci).

Jerin sunayen da aka dinga yaɗawar na ƙunshe da ƙasashen Masar, Pakistan, Indiya, da kuma Najeriya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *