Mutane 8 sun mutu bayan da Boko Haram ta dasa nakiya a babbar hanyar Maiduguri

Mutane 8 sun mutu bayan da Boko Haram ta dasa nakiya a babbar hanyar Maiduguri

An dan samu kwanciyar hankali tsawon wani lokaci a babban titin Damboa-Maiduguri a bangaren da ya shafi fashewar nakiyoyin a shekarar da ta gabata, in ji Zulum. Dakarun da ke yaki da ƴan Boko Haram sun rufe shanyar na  tsawon wata guda saboda dalilai na tsaro.

Gwamnan Borno ya na mai cewa “Za su tabbatar da ci gaba da zirga-zirga daga Maiduguri zuwa Damboa, hakan ba zai hana su bin hanyar ba.”

‘Yan Boko Haram da ‘yan ta’addar ISWAP na ci gaba da kai hare-hare a kan ayarin motocin.

Sun kara kaimi wajen dasa nakiyoyi a kan manyan tituna bayan an fatattake su daga yankunan da suka taba rikewa.

Da sanyin safiyar yau Asabar ne wata nakiya ta kashe soja daya tare da jikkata wasu hudu a lokacin da wata motar soji masu sulke ta bi ta kusa da garin Wulgo da ke kusa da kan iyaka da kasar Kamaru, in ji majiyar sojojin Najeriya.

Makonni biyu da suka gabata kungiyar ISWAP ta kai hari a wani sansanin soji dake Wulgo dake dauke da sojojin kasar Kamaru, inda suka kashe sojoji 25 tare da kona sansanin tare da daukar makamai da motocin yaki kamar yadda majiyoyin leken asirin Najeriya suka bayyana.

Zulum ya yi gargadin a makon da ya gabata cewa jihar Borno na fuskantar sake barkewar hare-haren mayakan Boko Haram.

 Sun kwato gundumomi uku a yankin tafkin Chadi da aka fatattake su.

Rikicin da ya faro tun a shekarar 2009 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40,000 tare da tilastawa kusan miliyan biyu barin muhallansu a yankin arewa maso gabas.

Rikicin dai ya barke a kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya, lamarin da ya kai ga samar da dakarun yankin da za su yaki mayakan.

rfi

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *