Gwamnatin jihar Kano ta kashe sama da Naira biliyan daya wajen siyan famfunan ruwa guda goma masu karfin gaske domin gyara tsarin samar da ruwan sha a jihar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa Umar Doguwa ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba injinan famfo a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa.
Doguwa ya yi karin haske kan matsalar karancin ruwa a Kano wanda ya sa Gwamna Abba Yusuf ya dauki kwakkwaran mataki.
“A matsayinsa na injiniya da kansa, gwamnan da kan sa ya tantance duk kamfanonin samar da ruwan sha a jihar ya kuma gano gurbacewar fanfunan ruwa a matsayin matsala ta farko” in ji Doguwa.
Ya yi bayanin cewa za a sanya fanfunan tuka-tuka guda shida kowanne mai karfin kilowatt 110 a cibiyar kula da ruwa ta Challawa yayin da za a sanya fanfunan tuka-tuka guda hudu kowanne mai karfin kilowatt 160 a cibiyar kula da ruwan ta Tamburawa.
Doguwa ya gargadi masana’antu da cibiyoyin kasuwanci da daidaikun mutane da ke cin zarafin ruwan sha musamman masu karkatar da shi zuwa ayyukan noma da su daina ko kuma su fuskanci fushin gwamnati.
“Mutane na sha’awar samun ruwan sha, amma duk da haka wasu mutane suna kai ruwa a gonakinsu ba bisa ka’ida ba.
“Muna binciken wadanda ke da hannu a ciki kuma idan ya cancanta za mu kwace filayen da aka samu da aikata irin wadannan ayyukan” in ji shi.
Ya kuma koka da batun satar ruwa inda mutane ke sintiri a cikin ruwan da ake amfani da su na gaggawa yana mai gargadin cewa ana ci gaba da aikin sa ido kuma duk wanda aka samu da aikata laifin za a hukunta shi.
Kwamishinan ya bukaci daukacin masana’antu da cibiyoyin kasuwanci a jihar da su daidaita kudaden ruwa cikin gaggawa yana mai jaddada cewa zamani na samun ruwan gwamnati kyauta ya wuce.
Ya bayyana cewa gwamnati ta fara aikin maido da ruwan bututun ruwa a garin Dambatta wanda ya shafe shekaru tara babu ruwan jama’a.
Doguwa ya tabbatar wa mazauna garin cewa an riga an samu gagarumin ci gaba, kuma nan ba da jimawa ba za a dawo da ruwan sha.
“Ba mu gaggawar wannan aikin ba muna son yin aiki mai inganci wanda zai jure gwajin lokaci. Da umarnin gwamna za mu tabbatar da cewa kowane gari a jihar Kano ya samu isasshen ruwan sha” inji shi.