Yayin da ake cika shekara 11 da sace ƴan matan sakandaren Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta yi a jihar Borno, har yanzu akwai ƴan mata 82 da ba su koma gida ba.
An sace ‘yan matan ne su 276 a ranar 14 ga watan Afrilun, 2014 – wannan mummunan al’amari na sace ƴan matan ya tayar da hankalin duniya a lokacin.
Mai magana da yawun ƙungiyar masu fafutukar ganin an saki sauran ƴan matan, Jeff Okoroafor, ya ce har yanzu iyayen waɗanda ƴaƴansu ba su koma gida ba na rayuwa cikin kunci.
Cikin abubuwan da ƙungiyar ke buƙata sun haɗa da; faɗa wa iyayen ƴan matan 82 da ƴaƴansu ba su koma gida ba ƙoƙari da ake yi na kuɓutar da su, da kuma fitar da rahoton Janar Ibrahim Sabo kan sace ƴan matan da kuma sanin irin matakin da gwamnati ta ɗauka ga waɗanda ke da hannu.
Sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta ce abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya ko kuma gazawar jami’an tsaro na ƙasa ceto sauran ƴan matan, shekara 11 da sace su – inda ta ce hakan ya nuna cewa gwamnati ba ta damu da ƴan ƙasarta ba.
“Muna jin ciwo duk lokacin da muka tuna sace ƴaƴan mu. Muna buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ganin ta ceto sauran ƴan mata, samar da tallafi ga waɗanda suka tsira da kuma hukunta masu laifi,” in ji sanarwar ƙungiyar.
Gwamnatin Najeriya dai ta sha yin alkawarin ceto sauran ƴan matan na Chibok, sai dai har yanzu babu labarinsu.