FAAC Ta Raba Naira Tiriliyan 15.26 Ga Asusun Tarayya Da Jihohi Da Kananan Hukumomi – Rahoton NEITI

FAAC Ta Raba Naira Tiriliyan 15.26 Ga Asusun Tarayya Da Jihohi Da Kananan Hukumomi – Rahoton NEITI

Kungiyar fayyace masana’antu ta Najeriya (NEITI) ta bayyana cewa kwamitin raba asusun ajiyar kudi na tarayya (FAAC) ya raba wa gwamnatin tarayya da jahohi da kananan hukumomi zunzurutun kudi har naira tiriliyan 15.26 da ba a taba ganin irinsa ba a shekarar 2024.

Wannan ya nuna wani babban tarihi na rabon kudaden shiga da kuma karuwar kashi 43% idan aka kwatanta da shekarun baya a cewar NEITI FAAC Quarterly Review da aka fitar a Abuja.

Rahoton ya danganta karuwar kudaden shigar da ake samu a kan tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta yi na yin garambawul a kasafin kudin kasar musamman cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin kudaden waje.

Wadannan tsare-tsare sun kara habaka kudaden shiga na man fetur wanda ya kasance babban sanadin karin kason.

Sakataren zartarwa na NEITI Dokta Orji Ogbonnaya Orji ya bayyana cewa an gudanar da binciken ne a daidai lokacin da wasu manyan sauye-sauyen kasafin kudi suka yi wadanda suka sauya fasalin kudaden shiga na Najeriya.

Ya jaddada muhimmancin tantance dorewar rancen da gwamnatocin tarayya da na Jihohi za su yi domin gudanar da ayyukansu da shirye-shiryensu da kuma abubuwan da ke tattare da dogaro da albarkatun kasa musamman ga jihohin da ke cin gajiyar kashi 13% na kudaden shigar da ake samu daga man fetur da iskar gas da ma’adanai.

Bayanan kasafi

Gwamnatin Tarayya: Ta karbi Naira Tiriliyan 4.95 karin kashi 24% daga Naira Tiriliyan 3.99 a shekarar 2023.

Gwamnonin Jihohi: Sun karbi Naira Tiriliyan 5.81, wanda hakan ya nuna an samu karin kashi 62% daga Naira Tiriliyan 3.58 a shekarar 2023.

Kananan Hukumomi: An samu Naira Tiriliyan 3.77 wanda ya karu da kashi 47% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Jimillar kudaden da FAAC ta fitar ciki har da kudaden shigar da ake samu, ya kai Naira tiriliyan 15.26 wanda ya nuna an samu karuwar kashi 66.2% daga Naira tiriliyan 9.18 a shekarar 2022 da kuma Naira tiriliyan 10.9 a shekarar 2023.

Manyan wadanda suka samu karbuwa: Jihar Legas ta samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 531.1 sai Delta (N450.4 biliyan) sai Rivers (N349.9 biliyan).

Mafi ƙanƙanci: Jihar Nasarawa ta samu mafi ƙarancin kason Naira biliyan 108.3 sai Ebonyi (N110bn) sai Ekiti (N111.9 biliyan).

Jihohi shida—Lagos Ribas da Bayelsa da Akwa Ibom da Delta da Kano—kowannensu ya samu sama da Naira biliyan 200 wanda ya kai kashi 33 cikin 100 na jimillar kudaden da aka ware wa duk jihohin.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *