Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sha alwashin kwato jarin ‘yan Najeriya da suka bata a cikin badakalar Naira Tiriliyan 1.3 da ake zargin wasu sun yi musayar kudi ta CryptoBank, inda ta yi alkawarin daukar mataki tare da hadin gwiwar Interpol da sauran hukumomin kasa da kasa.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels The Morning Brief, mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce a baya hukumar ta gargadi jama’a game da shirin Ponzi.
“Za ku iya tuna cewa a ranar 11 ga Maris na wannan shekara, Shugaban Hukumar EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya ba mu umarnin sanar da ‘yan Nijeriya kimanin kamfanoni 58 na Ponzi, mun fito da jerin sunayen – wanda ya nuna cewa muna da himma kuma muna lura da abinda ke abin da ke faruwa.
Ya kuma jaddada cewa CBEX wani kamfani ne na kasar waje da ke gudanar da ayyukan ta yanar gizo ba tare da wata doka ba a Najeriya.
“Duk ofisoshin yankin da mutane ke cewa suna cikin Ibadan ofisoshin baya aiki ba, duk abin yana kan intanet,” in ji shi.
Oyewale ya ci gaba da cewa, EFCC na hada kai da abokan huldar duniya domin gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
“Masu zuba jari za su iya samun kudadensu kuma mun riga mun fara aiki a kan hakan. Babu abinda zai shafi ‘yan nijeriya irin wannan ace babu wani abu da EFCC za ta iya yi a kai. A’a muna dauakr mataki na kwarewa,” in ji kakakin.
Source: Intel Region