Arsenal na zawarcin Guler, Madrid na shirin sakar wa Modric marar barin ƙungiyar
ANTALYA, TURKIYE - MARCH 13: Arda Guler of Fenerbahce celebrates after a goal during Turkish Super Lig soccer match between Aytemiz Alanyaspor and Fenerbahce at Bahcesehir Schools Stadium in Antalya, Turkiye on March 13, 2022. (Photo by Mustafa Ciftci/Anadolu Agency via Getty Images)

Arsenal na zawarcin Guler, Madrid na shirin sakar wa Modric marar barin ƙungiyar

Chelsea na ƙyalla ido kan ɗanwasan Bournemouth Dean Huijsen mai shekara 19 amma tana fuskantar gogayya daga sauran ƙungiyoyin Premier. (The Athletic – subscription required)

Ana kuma danganta ɗanwasan Real Betis Jesus Rodriguez mai shekara 19 wanda yake ƙarƙashin wata yarjejeniya ta kusan fam miliyan 42. (Mail)

Manchester United ta ƙara ƙaimi kan zawarcin golan Parma Zion Suzuki mai shekara 22 inda kulob ɗin Serie A ya yi wa ɗanwasan farashin fam miliyan 40. (Talksport)

Real Madrid a shirye take ta sakar wa gogaggen ɗanwasanta Luka Modric mai shekara 39 mara ya bar ƙungiyar a wannan bazarar. (Diario AS – in Spanish)

Inter Miami a shirye take ta yi tayin wata sabuwar yarjejeniya kan Lionel Messi mai shekara 38 da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas wanda kwantiraginsa ta ƙare a wannan bazara. (Mirror)

Arsenal na shirin yin tayin fam miliyan 35 kan ɗanwasan Real Madrid mai shekara 20 Arda Guler. (The Sun – subscription required)

RB Leipzig ta nuna sha’awar naɗa tsohon ɗanwasan Arsenal Cesc Fabregas wanda a yanzu yake jan ragamar Como a matsayin sabon kocinta. (Calciomercato – in Italian)

Manchester City da Bayern Munich da Borussia Dortmund na zawarcin ɗanwasan tsakiya na Barcelona mai shekara 16 Guille Fernandez. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Liverpool za ta nemi farashin tsakanin fam miliyan 17 zuwa fam miliyan 22 kan ɗanwasan gaba na Italiya Federico Chiesa inda AC Milan da wasu ƙungiyoyin Premier ke zawarcin ɗanwasan mai shekara 27. (Caughtoffside)

Daraktan gudanarwa na Bayer Leverkusen Fernando Carro yana da yaƙinin cewa koci Xabi Alonso da ɗanwasan Jamus mai shekara 21 Florian Wirtz za su ci gaba da zama a kulob ɗin a bazara. (Sky Sports Germany – in German)

Ana sa ran Manchester United za ta gabatar da tayi a hukumance kan ɗanwasan tsakiya na Atalanta Ederson mai shekara 25 inda kulob ɗin na Serie A ya ƙiyasta darajar ɗanwasan ɗan asalin Brazil kan kusan fam miliyan 52. (Tuttomercato – in Italian)

Liverpool na ƙara ƙaimi kan ɗauko ɗanwasan tsakiya na Inter Miami mai shekara 28 Nicolo Barella. (Fichajes)

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *